Wannan lokaci ne na shagalin murna ga dukkan iyalan Gidan, bayan a makon da ya gabata an ɗaura auren Gumsu Abacha a Gidan wanta Muhammad Abacha da ke Abuja.
Hajiya Maryam Abacha ta kasance mace mai kamar maza sakamakon jajircewa wajen kula da yaranta da tayi tun bayan rasuwar Mijinta Janar Sani Abacha shekaru masu yawa.
Allah ya albarkaci Maryam Abacha da ‘ya’ya 10, 3 Mata, Maza 7. Ita ce shugabar Matan Najeriya wato (First Lady) tun daga shekarar 1993 har zuwa 1998 lokacin da Mijin ta ya rasu.
Allah yajiƙan tsohon shugaban kasar Najeriya Janar Sani Abacha Amin.
Daga Kabiru Ado Muhd