
Tun bayan saukar Mai Martaba Khalifa Muhammadu Sunusi na II daga sarauta ne basaraken yaketa kara samun daukaka, domin kuwa basaraken ya zama khalifan Tijjaniya, wanda hakan yasa aka cigaba da bashi girma da daraja saboda wannan babban matsayi da ya samu.
Ba a iya Najeriya ba, har a kasashen waje ma ana martaba Khalifa Muhammadu Sunusi na II, domin kuwa ko a kwanakin baya da yaje kasar Ghana anga irin yadda aka martaba shi a kasar, domin kuwa irin tarbar da ya samu a kasar ko Shugaban kasa ne yaje sai haka. Tun daga ayarin jerin motocin da suka dauki basaraken daga filin jirgin sama zuwa masaukinsa za mu fahimci irin yadda yake da girma da mutunci da kima a wajen al’umar kasar ta Ghana.
A da lokacin da Khalifan Muhammadu Sunusi na II yake sarautar Kano idan zai fita ana yimasa rakiya da Algaita, Yanzu kuma da yake Khalifa idan zai fita ana yimasa rakiya da zakiri.
