Nilanshi Patel ‘Yar ƙasar Indiya ita ce aka karrama a matsayin wadda tafi kowa tsayin Gashi ta Duniya a 2020.

Nilanshi Patel wacce ake kiranta da Repunzel ‘ƴar asalin wani gari mai sunan ‘Modasa’ dake jihar Gujarat a ƙasar India ita ce hukumar ajiye kayyyakin tarihi ta duniya (Guiness world record) ta karrama a watan Janairu 2020 a matsayin yarinyar da tafi tsawon gashi a duniya.

Nilanshi Patel wacce take da shekaru 17 a duniya tayi shekaru 11 bata aske gashinta kanta ba sannan tsawon gashinta ya kai Santimita 190.

Shin shekaru nawa ka ke hasashen matanmu na nan za su kwashe kafin su tara irin wannnan gashin?

Daga Mutawakkil Gambo Doko

Leave a Reply

Your email address will not be published.