Abubuwan ban mamaki guda goma dangane da ƙasar ICELAND.

Iceland ƙasa ce ƙasar wuta da ƙanƙara, ta zama sanannen wurin tafiye-tafiye a cikin ƴan shekarun da suka gabata.

Daga kyawawan ƙanƙara na ƙasar, ruwa mai kwarara da kuma abubuwan almara na dare iri-iri.

Yana da sauƙi a ga dalilin da yasa matafiya ke tserewa zuwa ƙasar data kasance a ƙarshen duniya.

Akwai halaye da yawa wadanda suka sa wannan ƙasar ta zama ta daban, amma waɗannan abubuwan ban mamaki da ban sha’awa game da Iceland na iya ba ku mamaki. Fiye da misaltuwa. da:

1. Iceland ta tana da al’umma marasa yawa da basu fi wata ƙaramar hukuma ba a Najeriya. Kwata kwata yawan adadin mutanen ƙasar baifi adadin mutane 300,000.

2. Babban birnin ƙasar Iceland shine Reykjavik, amma alƙaluman lissafi sunyi amanna cewa, kaso sittin cikin ɗari na mutanen ƙasar suna rayuwa ne a babban birnin ƙasar wato Reykjavik. A babban birni otal otal, wajen shaye shaye, dakunan gidan tarihi da sai sauransu.

3. A Iceland anyi ittifaƙin cewa da akwai duwatsu masu aman wuta koda yaushe kimanin 125, wanda adadin su zai iya ƙaruwa dai dai da adadin aikace aikace da al’umma ƙasar keyi, da kuma ƙaruwar adadin su.

4. Wannan dalilin ne yasa a Iceland da akwai ƙoramu da kududdufai da ƙofar gida ma zakayi wanka aciki, kuma kududdufan na ruwan zafi ne bana sanyi ba, duk da akwai na sanyin. Ko zafi ko sanyi koda yaushe kududdufan suna da zafi, ba ruwanka da ɗumamawa.

5. Iceland itace ƙasa ta karshe a duniya da wani ɗan Adam yake raye.

6. Iceland ƙasa ce da take so kuma take daraja dabi’a ta karatu. Anyi ittifaƙin cewa a duk ƙasar Iceland, mutum ɗaya a cikin mutane 10 yana rubuta littafi.

7. Iceland ƙasa ce da bata da daji mai bishiyoyi. Kasa ce wacce ƙanƙara tayi wa katutu, saboda haka hazaƙa samu bishiyoyi ba barkatai. 8. Iceland basu da sauro, saboda haka basa fama da zazzaɓin maleriya ko kaɗan.

9. Ƙasar Iceland tana daya daga cikin ƙasa mafi tsaro a duniya. Ƙasa ce wacce yawan aikata laifi yayi ƙamfo.

10. Iceland basu da jami’an tsaro.

Shin yanayin ƙasar nan ya burge ka? Zakaso a ce Najeriya itama haka take kuwa? Bayyana ra’ayinka.

Shin yanayin ƙasar nan ya burge ka? Zakaso a ce Najeriya itama haka take kuwa? Bayyana ra’ayinka.

Rahoto: Abubakar Mustapha Kiru

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *