Zamantakewa
Yawaita tsotsar baki (kiss) yana rage ɓacin-rai a tsakanin ma’aurata. ~Masana

Daga | Ya’u Sule Tariwa,
Masana a fannin ilimin kimiyya sun bayyana cewa ma’auratan da suke yawaita tsostar bakin junansu (kiss) ba sa cika shiga ɓacin rai.
A wani littafi da masaniya kuma marubuciya, Sheril Kirshenbaum ta rubuta mai suna Science of Kissing, ta bayyana cewa a duk loƙacin da mutum ya kusanci abokin tarayyarsa da kiss, akwai wata sabuwar ƙauna da take shiga cikin zamantakewar ma’aurata.
Sannan yawaita tsotsar baki, ƴana ƙara danƙon soyayya tsakanin ma’aurata.
