Zamantakewa

Zamantakewar Matasa Kashi Na 02

Spread the love

Assalamu Alaikum Barkan mu da Saduwa a Wannan lokaci, a Cikin Shirin Mu Na zamantakewar Matasa Kashi Na Biyu.

Idan Mai Karatu Bai Manta ba, a Darasin Mu daya Gabata, Muna Magana akan Manyan Kalubale, Uku Masu Ciwa Matasa Tuwo a Kwarya.

Sune:
1-Matsalar Sana’a
2-Matsalar Karatu
3-Matsalar Aure

Idan muka Duba, Duka Wadannan, Matsalolin Suna komawa, Kan Matsalar Rashin Sana’a,
Da Rashin Sana’ar ne, Matashi ke kasa daukar Nauyin Kansa a Makarantar gaba da Sikandire, Jami’a ko kwalejin ilimi, idan ya Rasa mai Daukar Nauyin sa.

hakama Da Rashin Sana’a ne Matashi Kan Rasa, damar yin Aure Dakuma daukar Dawainiyar Yin Auren.

Wadannan Bangarori Guda Uku kowanne Matashi Yana Bukatar Su Domin Yazama Cikakken Dan Adam kamar kowa, Sana’a, ilimi da Aure.

A Ina Gizo Yake Sakar?

Abu Nafarko Da yakamata Mu Matasa, Mu Sani Shine Allah SWT Ya Halicci Dan Adam, Kuma ya Tsara Masa yanda zai Gudanar da Rayuwar sa, Hakanan Allah SWT ya Sanya Kalubalen Rayuwa, Su Zama Masu Bijiro Wa kowanne Dan Adam a kowanne Rukuni.

Misali tun daga Haihuwar Jinjiri yake Fara Cin karo da, irin Kalubalen Duniya, Rashin lafiya, Kumewar ciki Kokuma wani Abu Na daban, idan Mukayi Duba Ga Rayuwar Dan Adam Yana fara gwagwarmaya ne daga Ranar Da yazo Duniya har Zuwa Ranar komawar sa Ga Allah.
kowanne Rukuni Na Dan Adam Yana Fama da irin Nasa Kalubalen.

Mu kasa Rayuwar Dan Adam Kashi Uku Sa’annan Muleka kowanne Rukuni Mugani;

1-Jarirai/Yara(0-14 years)

2-Matasa(up to 35 years)

3-Dattijai(Ma’abota Shekaru)

Cikin kowanne Rukuni idan Mukayi Nazari da Tunani Zamuga Cewar Suna Fama da irin Nasu Kalubalen Rayuwar.

Rukunin Farko, Na Yara Na, Fuskantar Nasu Kalubalen Wanda Shine Fama da Cututtukan Yara, Sa’annan a Wasu Lokutan Fitowar wata gaba Ma ajikin su, Na Sanya su Jinya kamar, Hakori da ire-iren Su.

Haka abun Yake Ga Rukunin Dattijai Ma’abota Shekaru, Kan Fama da irin tasu Jinyar, Walau Ciwon Kafa, idanu, baya, Kokuma ire-iren Cutukan Zamani hawan Jini ko Cutar Sikari.

Hakama Abun Yake Ga Matasa Wanda Akan su muke Magana a Yanzu.

Matsalolin da Matasa Ke Fuskanta Kari Akan Ukun Damuka Lissafa a Baya; Matasa Kan Cin Karo Da Matsalar Rasa Jigo a Rayuwar Su Wato iyaye, Dayawa daga Cikin mu, Wasu Sun Rasa iyayen Su duka Biyu, Kokuma Daya Wanda Hakan ba karamin Radadi ke Sanya Matashi Yana ji Ba.

Da Wannan ne Zamu Fahimci Sunnar Allah SWT ta Jarabtar Bawan sa a kowanne Rukunin Rayuwar sa.

Aya ta 186 Cikin Ali’imran Allah SWT Yace:
لَتُبْلَوُنَّ فِي أَمْوَالِكُمْ وَأَنْفُسِكُمْ وَلَتَسْمَعُنَّ مِنَ الَّذِينَ أُوتُوا الْكِتَابَ مِنْ قَبْلِكُمْ وَمِنَ الَّذِينَ أَشْرَكُوا أَذًى كَثِيرًا وَإِنْ تَصْبِرُوا وَتَتَّقُوا فَإِنَّ ذَلِكَ مِنْ عَزْمِ الْأُمُورِ
(186) (آل عمران)

Lallai ne Za’a Jarraba ku, a Cikin Dukiyar ku, da Rayukan ku, Kuma Lallai ne kuna Jin Cutar Wa mai yawa daga Wadanda aka baiwa Littafi, Kafin ku, Dakuma Wadanda Sukayi Shirka. Kuma idan kunyi hakuri Kuma kukayi Takawa, to Lallai ne Yana daga Cikin Manyan Al’amura.

a Cikin de Surar Allah SWT ya Kara fada Mana:
يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا اصْبِرُوا وَصَابِرُوا وَرَابِطُوا وَاتَّقُوا اللَّهَ لَعَلَّكُمْ تُفْلِحُونَ (200) (آل عمران)

Ya ku Wadanda sukayi Imani, kuyi hakuri, Kuma kuyi juriya, Kuma kuyi zaman Dako(Tsaron ‘Yan Uwanku suna ibada) Kuma kuyi Takawa, tabbas Zaku Rabauta(Zakuci Nasara)

Zamu Dakata Anan Sai Kuma wani Mako idan Allah ya kaimu inda zamu yi Duba Ga Halin da Matasa Ke Ciki Na Rashin Samun damar Cikar Burikan Su.

Marubutan Shirin;
Daliban Jami’a a Bangaren Sociology Da Islamic Studies.

Shawarwarin Ku Ko Buqatar Tattaunawa Ku Tuntube Mu ta👇
Email:📧[email protected]

Ko Ta Whatsapp:07026746193

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button