ZAMANTAKEWAR””MATASA Kashi Na 01.

Zamantakewar Matasa Cike take Da Ababen Kalubale Dayawa Wanda Ya Shafi, Batun Neman Sana’a, Karatu Dakuma Soyayya, Da Aure.
Wannan Shiri Da Jaridar Mikiya ta Dauki Nauyin sa, Karkashin Dalibai Ma rubuta a Bangaren Sociology Da Islamic Studies, Manufar Shirin itace Samarwa Matasa Mafita a Rayuwar Su ta Hanyar Basu Shawarwarin Dasuka Dace Da Zamanin Da muke Ciki.
“”” MECECE ZAMAN TAKEWA”””
Zamantakewa na nufin tarayyar dan Adam, tsakaninshi da mutane yan uwansa da abokansa, kama daga lokacin da yake cin kuruciyar sa har girmansa,
Zamantakewa na farawa ne daga kuruciyar yaro, Sannan ya shiga samartaka har i zuwa dattijantaka , Alakar mutum da sauran yan uwanshi, ke nuna cikakkiyar dabi’ar Sa, yayin da yake ma’amalantar su ta Hanyar yin Magana da Aiki.
Dayake Muna Magana ne akan zamantakewar Matasa a Kasar Hausa Baki Daya, a Yau Zamuyi Duba da Sha’anin Sana’a ne a zamantakewar Matasa Wanda kowa Yasani Aikin Yi ko Sana’a Ga Matashi Shine Jigon Rayuwar sa.
a Da Can Baya kowanne Matashi Kan Tasowa Ne da Sana’ar gidan Su Misali; Dinki, Saka, Rini Dss.
Amma a Wannan Zamanin Damuke Ciki Babban Kalubalen Dayafi Ciwa Matasa Tuwo a Kwarya Shine Rashin Sana’a Kokuma aikin Yi,
Wannan Matsalar itace take Yin Tarnaqi Ga Rayuwar Matasa ta Bangorori Biyu;
Masu Muhimmanci Ga Rayuwar kowanne Matashi.
Nafarko Bangaren Karatun Sa
Nabiyu Bangaren Zamantowar Sa Cikakken Mutum ta Hanyar yin Soyayya Da Aure.
Sanin kowa ne Dukkan Abunda Muka Lissafa a Sama Abubuwa Ne Dake Buqatar kudaden Shiga Su kuwa Kudaden Shiga Basa Samuwa Sai da Aikin Yi Kokuma Sana’a.
So Dayawa matasa Mata Kan Korafin Rashin Fitowar Samarin su a Maganar Aure Dazaran Sunyi Musu Maganar Aure Sai Ruga a Guje Ba zasu Kara Ji ko Ganin Su ba, Yayinda Sukuma Matasa Maza Ke Kare Kansu Da Cewar Basu da Sana’ar Daza Su Iya Daukar Dawainiyar Soyayya Kokuma Aure, Amma a Zahiri Yake Matasan Kan Son Soyayyar da Auren Sai dai Kash Rashin kudaden Shiga Ne ke Kawo Musu Cikas.
Haka abun Yake Ma a Bangaren Karatu Musamman Ga Wanda iyayen Sa Su ka Zama Masu karamin Karfi Kokuma Suka Rigamu Gidan Gaskiya.
“”””a’ina Gizo Yake Sakar?
Mai Karatu Mu kasance Tare Daku a Shirin zamantakewar Matasa Na Ranar Juma’a Mai Zuwa Wanda Gungun Dalibai a Sociology Da Islamic Study Suke Gabatar Wa.
Domin Shawarwarin Ku Ko Buqatar Tattaunawa Daku Ku Tuntube Mu ta👇
Email:📧[email protected]
Ko Ta Whatsapp:07026746193