Kimiya Da Fasaha
Zamba Ta Yanar Giizo: EFCC Ta Aminta Da Zargin FBI.
Mai shari’a Oluwatoyin Taiwo na kotun manyan laifuka na jihar Legas, Ikeja ta yankewa Abiona Akinyemi Festus hukuncin daurin shekara biyu a gidan yari saboda yaudarar intanet.
Lauyan wanda Ofishin Ilorin Zonal na Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arziki Tu’annati (EFCC) ya tuhume shi da aikata laifuka biyu na satar bayanan yanar gizo yana cikin jerin sunayen Ofishin Bincike na Tarayya na Ma’aikatar Shari’a ta Amurka.