Zamu bawa Jami’an tsaro duk wani tallafin da suke bukata domin kawo karshen matsalar ta’addanci a jihar Kaduna ~Gwamna Uba sani.
Zababben gwamnan jihar Kaduna Sanata Uba sani ya sanar cewa ya zauna da hukumomin tsaro domin kawo karshen matsalar ta’addanci a jihar Kaduna Gwamnan ya bayyana hakan ne a wata sanarwa Daya fitar a shafinsa na Twitter Yana Mai cewa A yau, na jagoranci taron majalisar tsaro na sabuwar gwamnati ta. Taron wanda ya samu halartar Shugabannin Hukumomin tsaro domin samu bayanai kan matsalolin tsaro da suka hadar da ayyukan ‘yan fashi, garkuwa da mutane, rigingimun jama’a, sace-sacen jama’a, satar waya, barazanar karancin mai, fadan ‘yan kungiyar (sara suka) da kuma matsalar karancin wutar lantarki da ya dade a Jami’ar Ahmadu, Zariya. .
Na yi alkawarin baiwa hukumomin tsaro tallafin kayan aiki gaba daya domin su samu damar gudanar da ayyukansu yadda ya kamata. Shugabannin hukumomin tsaro sun tabbatar min da cewa sun jajirce wajen ganin an dawo da zaman lafiya a yankunan da ake fama da tashin hankali, musamman kananan hukumomi takwas Dake suka fi fama da wannan matsala dadai sauran su, tare da ci gaba da aiki a fadin jihar.
Wadanda suka halarci taron sun hada da shugabannin hukumomin tsaro kamar haka: Sojojin Najeriya, Rundunar ‘yan sandan Najeriya, Rundunar Sojan Sama, Ma’aikatar Tsaro ta Kasa, Makarantar Fasahar Makamai ta Sojojin Ruwa, Jami’an Tsaro da Civil Defence (NSCDC) da Jihar Kaduna. da ‘yan Bijilanti (KADVS).