Zamu Bawa ‘Yan Nijeriya Mamaki A Zaben Shugaban Kasa Na 2023, Cewar Jam’iyyar APC.
Jam’iyyar mai mulki ta sanar da wannan tabbaci ne bayan kaddamar da kwamitin sasanci nata a jihohin Imo da Ogun a ranar Juma’a, 21 ga watan Agusta, a Abuja, jaridar Daily Trust ta ruwaito.
Da yake magana kan ci gaban, Shugaban kwamitin rikon kwarya na APC, Gwamna Mai Mala Buni na jihar Yobe ya bayyana cewa bayan sasancin, su kansu fusatattun mambobi za su dawo jam’iyyar sannan su taimaka wajen karfafata gabannin zaben 2023.
Gwamna Buni ya bayyana cewa APC za ta shayar da fannin siyasar Najeriya mamaki da dawowar manyan tsoffin jiga-jiganta.
Da yake nuna farin ciki a kan sabuwar yunkuri na jam’iyyar, sabon shugaban na APC ya ce:
Bari na kara da fadin cewa wannan shiri na sasanci da ke gudana a jam’iyyar All Progressives Congress (APC) zai shayar da mamaki kwanan nan a fannin siyasar Najeriya da dawowar tarin tsoffin mambobin jam’iyyar da suka fusata sannan suka barta zuwa wasu jam’iyyun ba tare da sun so ba.