Zamu fara tantance daliban jihar Kano domin Kai su kasashen waje bisa tsarin tallafin karatu ~Cewar Abba Gida-Gida.

Gwamnan jihar Kano Engr Abba Kabir Yusuf ya bayyana dawo da tsarin bayarda tallafin Ilimi ga Yan Jihar Kano gwamnan da Kansa ya bayyana hakan a shafinsa na Facebook Yana Mai cewa A cikin jawabin da na gabatar ranar rantsuwa, na bayyana cewa mun dawo da tsarin nan na cigaba da bayar da tallafin karatu ga ɗaliban mu na jihar Kano domin samun manyan digiri a cikin gida da ƙasashen waje. A cikin watanni masu zuwa, za a fitar da ƙarin bayani, kuma za a fara aikin tantancewa domin fara wannan aiki.
Haka kuma, za a buɗe makarantun fasaha guda 44 da Makarantun koyon Ilimin Addinin Musulunci guda 44 da ke fadin kananan hukumominmu da Gwamnatin Sanata Kwankwaso ta kafa, wadanda gwamnatin da ta gabata ta rufe kuma ta yi watsi da su domin ci gaba da karatu da. – AKY