Labarai
Zamu gyara social media a maimakon mu rufe ta
Ministan Yada Labarai da Al’adu, Lai Mohammed, a ranar Alhamis ya ce matsayin Gwamnatin Najeriya game da makomar kafofin sada zumunta a kasar nan Yace tsari ne za’ayi a maimakon rufe shi. Mohammed ya bayyana hakan ne a wani taron manema labarai a Abuja.
Ministan ya yi ikirarin cewa an yi amfani da kafofin sada zumunta ta hanyarsa ba daidai ba don haifar da hargitsi a Lokacin Zanga Zangar #ndSARSprotest.
Ya ce gwamnati za ta yi aiki ne kawai da masu ruwa da tsaki don daidaita ayyukan kafofin sada zumunta a kasar.
Tuni ‘yan Najeriya suka yi watsi da shirye-shiryen da gwamnati ke yi na daidaita kafafen sada zumunta, suna mai cewa hakan zai tauye‘ yancin ‘yan kasa na fadin albarkacin baki.