Labarai
Zamu hukunta duk wanda ke da hannu kan kisan ‘Yan Maulidi a jihar Kaduna – Tinubu
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya tabbatar wa al’ummar kasar cewa duk wanda aka samu da hannu a harin bam a kauyen Tudun Biri wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane sama da 90, za a hukunta shi.
Shugaban ya kuma ba da tabbacin cewa za a kula da duk wadanda abin ya shafa a karkashin shirin Folako Initiative da za a fara a wannan watan.
A cewarsa, al’ummar za ta kasance al’umma ta farko da za a sake ginawa a karkashin sabon tsarin.
Mataimakin shugaban kasa Kashim Shattima ya wakilce shi ne ya bayyana hakan a ranar Alhamis jim kadan bayan ya ziyarci wadanda lamarin ya rutsa da su a asibitin koyarwa na Barau Dikko domin jajanta musu bisa wannan mummunan lamari.