Labarai

Zamu sake kulle iyakokin Nageriya matukar ‘yan Nageriya Basu kiyaye ba ~Garba Shehu.

Spread the love

Babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa Muhammadu Buhari kan harkokin yada labarai, Garba Shehu, ya yi gargadin cewa Batun iyakokin Najeriya da aka sake budewa a makon da ya gabata za a iya sake rufe su idan akwai “matsala”.

Shehu ya bayyana hakan ne a ranar Talata yayin da yake jawabi a shirin Siyasar Yau na gidan Talabijin din Channels.

Gwamnatin Tarayya ta ba da umarnin sake bude kan iyakokin Jihar Legas, da Illela da ke Jihar Sakkwato, da Maigatari da ke Jihar Jigawa, da kuma Mfun da ke Jihar Kuros Riba daga ranar 16 ga Disamba.
Dukkansu an rufe su a watan Agusta 2019, yayin da Najeriya ke neman hana shigo da magunguna ba bisa ka’ida ba, kananan makamai da kayan gona daga kasashen Afirka ta Yamma makwabta.

Wani kwamiti na shugaban kasa wanda aka kafa akan lamarin ya kammala aikinsa kuma ya bada shawarar bude kan iyakokin.

Amma Shehu a yanzu ya koka kan yadda makwabtan Najeriya ba su ba da hadin kai ga kasar ba don takaita kwararar ‘yan fashi da kananan makamai.

“Mun sake budewa ne da fatan cewa yarjejeniyar da muka kulla da su, za su yi aiki kafada da kafada da hukumomin tsaronmu, tare da kwastan namu, a kan gwaji, saboda ba a bude dukkan wuraren shiga ba. Za a gwada shi, idan ya yi aiki sosai, to za a sake buɗe wasu. Idan akwai matsala, to gwamnati na iya sake tunani.

Kwamitin fasaha ne zai ba gwamnati shawara kan yadda abubuwa ke tafiya yanzu tunda mun sake bude guda hudu daga cikin adadin da muke dasu, ”in ji Shehu

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button