Labarai

Zamu Samarwa Yan Najeriya Aikin Yi Miliyan 5, Inji Mataimakin Shugaban Kasa Osinbajo.

Spread the love

Daga Comr Yaseer Alhassan

Mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo ya bayyana cewa zasu samarwa da matasan Najeriya ayyukan yi Miliyan 5.

Ya bayyana hakane a wajan wata ganawa da aka yi dashi ta kafar sadarwar Zamani inda yace dama gwamnatinsu daya daga cikin muhimman manufofinta sune samar da ikin yi.

Yace suna baiwa bangaren aikin Noma da samar da abubuwan amfanin yau da kullin da kuma gina gidaje muhimmanci, Osinbajo yace zasu fara amfani da Siminti wajan gina tituna saboda ya fi sauki da kuma karko.

Ya kuma bada tabacin cewa gwamnati zata karfafawa kananan Masana’antu.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button