Labarai
Zamu tura dubu takwas-takwas ga gidajen talakawa milyan sha biyu na tsawon watanni shida ~Shugaba Bola Tinubu.
Hakan na kunshe ne a cikin wata wasika da shugaban kasar ya rubutawa majalisar wakilai dangane da bukatar gwamnatin Buhari ta ciwo bashin dala miliyan 800 domin shirin samar da tsaro na zaman lafiya.
Shugaban kasar na neman amincewar majalisar ne domin samun lamunin.
A cewar shugaban kasar, tura kudaden ga magidanta marasa galihu zai yi tasiri mai yawa akan mutane kusan miliyan 60.
Don tabbatar da gaskiya, Shugaban ya ce za a tura kudin zuwa gidaje ta hanyar fasahar zamani dijital.