Kungiyoyi

Zamucigaba Da Ayyukan Jinƙai a Najeriya Inji YCAPF.

Spread the love

Ƙungiyar Matasa masu fafutukan samar da zaman lafiya da Cigaban Al’umma ta Najeriya (Youth Crisis Awareness and Peace Forum YCAPF) Reshen Jihar Kano takai ziyara ta musamman Gidan Marayu ta Nasarawa a Ƙwaryar Kano.

Ziyaran tazo ne Albarkaci ranar Jinƙai ta Duniya Wadda Majalissar Ɗinkin Duniy(MDD) ta ware kowacce 19/Agust na kowacce shekara,(International Humanitarian Day).

A wannan Rana Mai Albarka Ƙungiyar YCAPF reshen jihar Kano ƙarƙashin Jagorancin shugabanta na Jiha Amb Anwar Waisu (Born Legend) takai ziyarar ƙafa da ƙafa zuwa gidan Yara dake Nasarawa a ƙwaryar birnin jihar Kano.

Wannan ziyarar ta ƙunshi Cin abinci Rana tareda wannan yaran dake gida da Kuma rabamasu kayan abinci dana Sawa da Omo da Sanitiser da dai sauransu.

A yayin ziyarar wannan ƙungiya ta sami tarba mai kyau daga shugabar wannan gida tareda muƙararrabanta. Shugabar tayi jawabin nuna farinciki da bada taƙaitaccen tarihin wannan gida.

Gidan Marayu na Nasarawa anfara Shi ne cikin shekarar 1957 a Burma wanda take cikin Sabon gari a yanzu, gidan Marayun ya fara ne da gado biyu (2) ,da Kuma Yara guda hudu(4), ta hannun wata Baturiya Ƴar asalin Ƙasar Amurka mai suna Mrs Juliet Kuma tayi Kamar shekaru 10 tana Jagorancin wannan tafiyar kafin a shekarar 1967 zuwan Gwamna Audu Bako ya dawo da gidan ƙarƙashin ikon Gwamnati, Wanda har yanzu yana ƙarƙashin iko na Gwamnati.

A shekarar 1968 ya dauko gidan daga Burma zuwa wannan gidan dake Nasarawa, Kuma tayi Kira ga Al’umma da suzo su dinga taimakawa yaran nan domin Suma su Sami jindadin zaman duniya.
Bayan jawabin Shugabar ta zagaya cikin gidan tareda mambobi na YCAPF kuma sukayi duk abinda yakaisu wannan gida.
Daga karshe ƙungiyar YCAPF ta Mika godiya tayi Sallama.

Ita dai wannan rana ta Jinƙai tun a 2009 ne MDD tare domin tunawa da masu bada Agaji da aka kashe a ƙasar Iran sakamakon ayyukan jinƙai.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button