Zan Amsa Gayyatar DSS Ghali Na’Abba.
Daga Comr Yaseer Alhassan Gombe
Tsohon kakakin majalisa, Ghali Na’Aba ya ba ya bada tabbacin zai girmama gayyatar da hukumar DSS tayi mai zuwa hedkwatarta da ke Abuja da karfe 12 na rana ranar Litinin don amsa tambayoyi kan hirar da ya yi ta gidan talabijin da yayi makon da ya gabata.
Na’Abba ya yi magana a matsayinsa na mai matsayin shugaban kwamitin tuntuba na kasa (NCF), kungiyar da take da nufin kafa gwamnatin hadaka.
Sanarwar daga Shugaban Ofishin NCF, Dakta Tanko Yunusa ya ce Na’Abba zai girmama goron gayyatar, duk da cewa ya nuna cewa sannu a hankali kasar na karkata zuwa ga ” kasar yan sanda ‘.
Yayin hirar, Na’Abba yayi magana game da shirin NCF “don kawo sabuwar Najeriya wanda zaiyi aiki ga kowa”.
Tsohon shugaban ya zargi gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari da gazawa.
Ya ce gwamnati ta gaza kawo karshen rashin aikin yin matasa da rashin tsaro da ke haifar da kashe-kashen ‘yan Najeriya a kullum.
Ya ce bashin kasar ya yadu a karkashin gwamnatin kuma talauci ya karu a tsakanin ‘yan Najeriya.