Labarai

Zan ci gaba da ha’da hannu da Kungiyoyin kiyon lafiya na duniya domin samun ingancin kiwon lafiya a Nageriya ~Shugaba Tinubu.

Spread the love

Shugaba Bola Tinubu ya ce gwamnatin tarayya za ta ci gaba da hada hannu da kungiyoyi masu inganci don samar da ingantaccen kiwon lafiya ga daukacin ‘yan Najeriya.

Tinubu ya kara da cewa, manyan kungiyoyi irin su Rotary International abokan hadin gwiwa ne na gaske a kokarin da ake na kawar da duk wani nau’in cutar shan inna da kuma rage yawaitar mace-macen mata da jarirai a kasar nan.

Shugaban ya bayyana haka ne a lokacin da ya karbi bakuncin shugaban Rotary International, Mista Gordon McLnally, matarsa, Heather; Jakadan Rotary na Polio a Najeriya, Sir Emeka Offor; da sauran fitattun ‘yan Rotars a ranar Juma’a a Abuja.

Ya yabawa kungiyar kan ayyukan da ta ke yi a fannin kiwon lafiyar kasar nan, da suka hada da sabon tallafin dala miliyan 14 domin baiwa hukumar lafiya ta WHO taimakon fasaha ga gwamnatin Najeriya kan sa ido kan cutar shan inna.

Kungiya “Rotary International tana da kyakkyawan suna wajen sadaukar da kai ga al’umma, ba wai kawai ga rawar da ta taka wajen kawar da cutar shan inna a Afirka ba, har ma da magance wasu cututtuka.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button