Labarai

Zan fitar da ‘yan Nageriya Milyan dari 100 daga talauci, Karya ce

Spread the love

Wani jigo a Jam’iyar New Nigerian Peoples Party, (NNPP), Olusegun Bamgbose, ya bayyana sanarwar da Shugaba Muhammadu Buhari ya yi na fitar da ‘yan Nijeriya miliyan 100 daga kangin talauci a matsayin tsantsar karya, rashin gaskiya da Kuma cin Amana Ku tuna cewa Buhari, a cikin jawabin sa na baya-bayan nan, a wurin komawa Minista, Sakatarorin din-din-din da sauran manyan jami’an gwamnati, ya sanar da ‘yan Nijeriya shirye-shiryen gwamnatin sa na fitar da‘ yan kasa miliyan 100 daga talauci a cikin shekaru 10 masu zuwa.

Wannan shirme ne kawai. da rashin gaskiya. Hakan daidai yake da bai wa ‘yan Najeriya zuman na karya,” in ji babban lauyan a tattaunawarsa da Daily Post a ranar Juma’a. “Daya daga cikin Ministocin sa ya taba fada mana cewa kusan‘ Yan Najeriya miliyan 90 ke fama da talauci, ta yaya Shugaban kasa zai fada mana yanzu cewa zai fitar da ‘Yan Najeriya miliyan 100 daga kangin talauci? “Ta yaya za samu ƙarin Najeriya miliyan 10?” . Bamgbose ya ce wannan manuniya ce cewa kalaman ba su cancanta ba amma kawai an yi shi ne don siyasa don yaudarar ‘yan Nijeriya da ba su day wayo alhali kuwa babu wani cikakken shiri Wanda suka cimma a karshe Yayi gargadi ga Shugaban kasa da ya daina ba wa’ yan Najeriya Labarin na karya.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button