Labarai

Zan Kasance A Tare Daku Koyaushe, Inji Atiku

Spread the love

Tsohon Mataimakin Shugaban Najeriya, Atiku Abubakar, ranar Talata, ya tabbatar wa matasan Najeriya cewa a shirye yake ya kula dasu a cikin yanayin dadi ko na wuya.

Atiku ya bayyana hakan ne a yayin bikin cikar shekara 20 da ranar matasa ta duniya, IYD, 2020.

A cikin sakon da ya sanya wa hannu, Wazirin Adamawa ya umarci matasa da su dage kan kokari ganin kasa Najeriya ta cigaba.

Ya ce: “Ina taya murna ga matasa a duk fadin duniya na zagayowar ranar matasa 20. “Zamu cigaba da aiki dasu kafada kafada da kowa, saboda a matsayinku na matasa, ku“ Shugabannin gobe”. “Ina gode ga matasan Najeriya musamman saboda kwazonsu da jajircewarsu don ganin Najeriya ta samu daukaka. “

Taken bikin na bana ” Hadin Kan Matasa don Cigaban Duniya ”.

Bikin ya ba da mahimmanci game da abin da duniya ta tsinkaye game da gungun matasa a duniya.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button