Labarai
Zan Marawa Peter Obi baya a zaben 2027 idan ~Cewar Atiku Abubakar


Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya bayyana cewa zai goyi bayan dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour a 2023, Peter Obi, idan jam’iyyar Peoples Democratic Party ta yanke shawarar cewa Kudu maso Gabas su ne da damar a 2027.
Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP a zaben 2023, Atiku, ya ce zai yi watsi da takardar sa ya goyi bayan Obi idan jam’iyyarsa ta zabe shi.
Tsohon mataimakin shugaban kasar ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi da Sashen Hausa na BBC a baya-bayan nan, inda ya kara da cewa ya yi yunkurin zama shugaban kasa ne a shekarar da ta gabata saboda an zabe shi a jam’iyar PDP domin takarar.