Labarai
Zan tabbatar da cewa an daina dauke wuta a Najeriya idan na zama ministan wuta ~inji El-Rufai


Tsohon Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufai ya ce babban abunda zai sanya a gaba idan ya zama minstan wuta shine kokarin ganin an samu tsayayyar wuta a Najeriya domin dukkan wani cigaba na Najeriya ya dogara ne da wutar lantarki
Jaridar Wakiliya ta ruwaito A lokacin da El-Rufai ke cewa wanda ke amsa tambayoyi a gaban majalisar dattawa yace zai yi maganin masu satar wuta wato bye-pass sannan zai karbo kadarorin wutar lantarki da aka sayar irinsu DISCO dake da alhakin samar da wutar da dai sauransu, “nan da shekara bakwai sai wutar Najeriya ta inganta idan na zama minsta in sha Allah idan” inji El-Rufai