Labarai

Zanga-zangar tsadar rayuwa ta ɓarke a Minna babban birnin jihar Neja

Spread the love

Masu zanga-zangar sun ce tsadar kayan abinci da kuma rashin kokarin da gwamnati ke yi na kame lamarin ya tilasta musu toshe manyan tituna.

Mazauna Minna, babban birnin jihar Neja, a ranar Litinin, sun gudanar da zanga-zangar nuna adawa da tsadar rayuwa a kasar, tare da toshe manyan tituna a cikin birnin.

An ji masu zanga-zangar da suka hada da mata da matasa suna rera wakokin zanga-zangar, yayin da jami’an tsaro ciki har da ‘yan sanda suke lura dasu.

Masu zanga-zangar sun ce tsadar kayan abinci da kuma rashin kokarin da gwamnati ke yi a lamarin ya tilasta musu rufe manyan tituna domin gwamnati ta ji kukansu.

Mataimakin gwamnan jihar Neja, Yakubu Garba, a lokacin da yake jawabi ga masu zanga-zangar, ya ce gwamnati na sane da kuncin rayuwa da iyalai ke fuskanta a wannan lokaci.

Ya ce gwamnati na kokarin rage tsadar rayuwa da sakamakon cire tallafin man fetur

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button