Zanyi mulki irin na Marigayi Umaru Musa ‘Yar-Adua – Tinubu
Zababben shugaban kasa, Asiwaju Bola Tinubu a ranar Juma’ar da ta gabata ya yaba wa marigayi shugaban kasa Umar Musa ‘Yar’Adua bisa jajircewarsa na tabbatar da dimokuradiyya da shugabanci na gari, inda ya yi alkawarin bin matakan da ya dauka.
A wata sanarwar da Tinubu ya sanya wa hannu, zababben shugaban kasar ya ce Marigayi Yar’Adua ya yi rayuwa mai ma’ana.
Yace; “Ba Za Mu Taba Mancewa da Ku ba! A yau, kamar kullum, ina tunawa da abokina kuma dan uwana na kwarai a fafutukar tabbatar da dimokuradiyya da shugabanci na gari a Nijeriya, marigayi Shugaba Umaru Musa Yar’adua, wanda ya rasu a rana irin ta yau shekaru 13 da suka gabata.
“Mayu 5, 2010 mai yiwuwa ta daɗe amma, ga wasunmu, raunin har yanzu sabo ne. Muna tunawa da ranar kamar yadda muke tunawa da rayuwa mai ma’ana da Mallam Umaru Yar’Adua ya yi.
“A matsayina na abokinsa kuma dan siyasa ina mutunta abubuwan da suka faru na gaskiya, dagewa, kishin kasa da kuma nagartar aikin gwamnati wanda Marigayi ‘Yar’aduwa ya bari a matsayin gwamnan jihar Katsina (1999 zuwa 2007) da kuma shugaban Najeriya (2007 zuwa 2010).
“Yayin da nake shirin karbar ragamar shugabancin kasar nan a ranar 29 ga watan Mayu, na kuduri aniyar yin koyi da kyawawan misalai da shugabaci irin su Malam Umaru ‘Yar’adua suka bayar wadanda suka nuna nagarta ta kwarai da kuma sadaukar da kai ga kasarmu mai daraja.