Rahotanni

Zanyi Manyan Ayyuka Guda 9 Wadanda Dukkan ‘Yan Kasa Zasu Amfana Kafin Nabar Mulki~Buhari.

Spread the love

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari yayi Ikirarin samar da wasu Abubuwa guda tara da zai Amfani `Yan Kasar a Cikin Shekaru 3 da suka rage masa a Karagar Mulki.

Abubuwan da Buhari yayi alkawarin zai kawo Sune Kamar Haka:-

1 Gina tattalin arziki mai dorewa

2 Bai wa jama’a dama da yaye talauci

3 Inganta sha’anin noma domin samar da abinci har ma a rinka fitar da shi

4 Samar da wutar lantarki tsayayya

5 Samar da ingantaccen sufuri

6 Inganta sana’o’i da masana’antu

7 Samar da ilimi mai nagarta

8 Samar da ingantacciyar lafiya ga ‘yan kasa a farashi mai rahusa

9 Fito da hanyoyin yaki da rashawa da cin hanci da kuma inganta harkar tsaro.

Sai dai wasu Na ganin wannan Abin tamkar Almara, Inda suka dogara da cewa Shugaba Buhari ya kasa Cika Alkawari ko daya Cikin alkawura 3 da ya Dauka cikin Shekaru 5 da yayi a karagar Mulki.

Idan baku mantaba Shugaba Buhari, a lokacin yakin Neman Zabensa Yayi, Yakin neman zaben ne da Alkawura guda uku ga `Yan Kasa Inda yace:-

1_Zai Inganta Tsaro

2_Zai Yaki Cin hanci da Rashawa

3_Zai Samar da Aiyuka ga Matasa, Ya Kori zaman Banza a Kasar.

Wasu na Ganin Buhari bai cika wannan alkawari cikin shekaru biysr ba, Sannan Yace zai yi Guda tara cikin Shekaru 3 abin Kamar ba mai yuwuwa bane ga Ra’ayin wasu `yan Kasa.

Ahmed T. Adam Bagas

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button