Kasuwanci

Zargin Ɗaukar Nauyin Ta’addanci: CBN ya bada umarnin rufe asusun masu amfani da kuɗin intanet na crypto currency.

Spread the love

‘Yan Arewa masu harkar crypto currency akwai matsala.

Babban bankin Najeriya CBN ya umarci bankunan ƙasarnan da su rufe duk wani asusun ‘yan kasuwa da kamfanoni masu amfani da kuɗin nai ntanet crypto currency.

Umarnin na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da babban bankin ya fitar a yau juma’a ga bankunan hada hadar kuɗi DMB da kamfanonin da ba na harkar kuɗi ba MBFI da kuma sauran ma’aikatun harkokin kuɗi.

Ƙarin umarnin da aka bayar tun a baya CBN yana tunatar da ma’aikatun da ke mu’amulla da kuɗaɗen intanet ko kuma dillalansu cewa haramun ne.

Saboda haka an umarci MBFIs da OFIs da su tantance irin mutanen da ke amfani da irin waɗannan kuɗaɗen sannan su rufe asusun ajiyar nasu.

Tun a shekarar 2017 CBN yace kuɗaɗen bitcoin da litecoin da sauran su ana amfani da su ne wajen ɗaukar nauyin ta’addanci da halasta kuɗin haramun saboda ganin cewa ba a iya bin sahunsu.

Kazalika tun a 2018 CBN ya ce kuɗaɗen ba sa cikin waɗanda mai su zai iya kai ƙara kotu don neman haƙƙinsa a Najeriya.

Daga Kabiru Ado Muhd.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button