Labarai

Zargin Cin Amana: Wani Magidanci Ya Rataye Kansa Bayan Ya Kashe Matarsa.

Spread the love

Daga Comr Yaseer Alhassan Gombe

Wani magidanci da a ka bayyana shi da suna PrideHove ya rataye kansa bayan ya sheke matarsa bisa zargin cin Amana.

A rahoton da jaridar iHarare dake a kasar Zimbabwe ta rawaito ta bayyana cewa, Matar Mutumin mai suna Patience Matura tun da fari, ta karbi wani sakon kartakwana mai dauke da kalaman soyayya wanda hakan ne ya fusata mijin nata.

Wani Makoci ga Ma’auratan sai da ya shafe kusan a wanni biyu yana sulhunta su, amma, Inaaaa magidancin sam bai hakura ba, har ta kai ga ya Illata matarsa, wanda yayi sanadin mutuwarta, sa’annan shima ya je ya rataye kansa.

Hukumar ‘yan sanda dake Kasar Zimbabwe ta bakin Mai magana da yawun hukumar Joel Goko, ya tabbatar da faruwar al’amarin.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button