Labarai

Zargin Cin Hanci A Hukumar Yaki Da Cin Hanci Ta EFCC Yasa An Dakatar Da Wasu Manyan Jami’ai.

Ashe Dai Ba Magu Ne Kadai Mai Laifi Ba: Shugaba Buhari Ya Dakatar Da Dukkan Manyan Jami’an EFCC.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dakatar da wasu manyan jami’ai 10 na Hukumar Yaki da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC.

Kafar yada labarai ta PM News ta nakalto wata majiya a fadar shugaban kasa a daren Talata tana cewa Sakataren zartarwa na hukumar Olanipekun Olukoyede na daga cikin manyan jami’an da shugaba Buhari ya dakatar.

An dakatar da su ne saboda wasu laifuffuka daban-daban da ake zarginsu da aikatawa, inji majiyar.

An dakatar da su ne don ba da damar bincike na gaskiya game da zarge-zargen cin hanci da rashawa da ke damun hukumar hana cin hanci da rashawa.

Majiyar ta kara da cewa An dakatar da dukkan manyan jami’ai a hukumar, an kulle ofisoshinsu, don hana duk wata matsala da fayiloli a hukumar.

Majiyar jaridar ta ce sabon mukaddashin Shugaban hukumar ya tsira daga dakatarwar, saboda an same shi ba ya cikin wadanda ake zargi da mu’amala da su a cikin hukumar.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button