Labarai

Zargin damfara daga APC sarki ya nisanta kansa

Babu abin da zan yi da wanu Hushpuppi – Bukola Saraki

Tsohon Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki ya karyata batun yana da wata alaqa da mutumin da ake zargi da aikata laifin satar yanar gizo, Ramon Abbas wanda aka fi sani da Hushpuppi idan baku manta ba dai jam’iyyar All Progressives Congress (APC) take danganta shi saraki da atiku da Hushpuppi sai dai saraki yace yana kallon zargin na APC a matsayin mara ma’ana da kuma Sharrin siyasa na APC. A kwanakin baya an kama Hushpuppi a Dubai kuma aka tura shi Amurka saboda zargin sa da hannu a hada-hadar kudade da kuma ayyukan yanar gizo.

A cikin sanarwar da jam’iyyar ta APC ta fitar a ranar Asabar, ta zargi Jam’iyyar PDP da suka hada da tsohon Mataimakin Shugaban kasa Atiku Abubakar, Tsohon Kakakin majalisa Yabuku Dogara, Saraki da Sanata Dino Melaye da yin hulda da wanda ake zargi da aikata laifin satan yanar gizo. A cikin sanarwar da Saraki ya fitar a cikin wata sanarwa a Abuja ta hannun mai taimaka masa kan harkokin yada labarai, Yusuph Olaniyonu, ya ce ba shi da wata alaka da Hushpuppi kuma ba ya san shi ta kowace hanya ba. Ya ce: “Maganar da aka yiwa APC, jam’iyya mai mulki a kasarmu, tana daya daga cikin masu hana dm hukumominmu yaki da cin hanci da rashawa don haka yanzy anyi walkiya APC bata da wata bakin magana an gano makaryata ne…

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button