Labarai

Zargin Wawure Kudaden Al’umma Da Sunan Corona, ICPC Zatayi Bincike.

Spread the love

Korafe-korafe sunyi yawa akan yadda gwamnatoci Suke kashe kudade da sunan Corona, sabili da haka ne Hukumar Yaki da Cin Hanci ta ICPC tace zata fara bincike akan yadda Gwmnati ta kashe kudaden da sunan Corona.

A wata sanarwa mai dauke da sa hannun Shugaban ayyuka na hukumar ta ICPC Akeem Lawal, ta bayyana cewa hukumar ta fara bincike akan zarge-zargen al’mundahana da wasu bangarorin hukumomin Gwamnati sukayi wajen rabon tallafin, da Kuma zargin rashawa wajen sayo kayan tallafin da kudaden zirga-zirga, da kuma kudaden da aka kashe wajen wayar da kan al’umma game da cutar ta Corona.

Lawal ya ce akwai jihohin da suke bincike, wadanda gwamnatoci suka handume kudin kananan hukumomi da sunan annobar, sannan akwai kuma jihar da aka karkatar da kudaden tallafin, wanda aka rasa inda aka kaisu.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button