Labarai

Zazzabin Cizon Sauro ya kashe Sama da mutun dubu dari takwas 800,000 a jihar jigawa.

Spread the love

Shugaban babban asibitin gwamnati dake Dutse, jihar Jigawa Abbas Ya’u ya bayyana cewa yara ƴan ƙasa da shekaru biyar, 121 sun rasu a cikin watanni hudu a jihar a dalilin fama da suka yi da zazzabin cizon sauro.

Ya’u ya fadi haka ne da yake hira da majiyarmu ta PREMIUM TIMES.

Alkaluma sun nuna cewa a tsakanin wadannan watanni hudu da aka rasa Yara 121 suka mutu duk wata asibitin kan rasa yara 30 a dalilin zazzabin cizon sauro.

Zazzabin cizon sauro

Zazzabin cizon sauro cuta ce da ake kamuwa da ita a dalilin cizon sauro da ake kira ‘female anopheles mosquitoe’.

Alamun cutar sun hada da ciwon gabobin jiki, zazzabi, amai, rashin iya barci, ciwon kai, Suma, da dai sauran su.

Kungiyar kiwon lafiya ta duniya WHO ta ce cutar kan yi ajalin mutum ko ta jirkitar da kwakwalwar mutum ko Kuma ta tsotse jinin mutum Idan ba a gaggauta neman magani da wuri ba.

Sakamakon rahoton da ‘World Maleria’ ta gabatar a Disemba 2019 ya nuna cewa mutum miliyan 228 ne suka kamu da zazzabin cizon sauro a shekaran 2018 sannan a 2017 mutum miliyan 231 a duniya.

Sannan kuma rahoton ya nuna cewa cutar ta yi ajalin mutum 405,000 a shekaran 2018 sannan a 2017 mutum 416,000.

Bayan haka Nahiyar Afrika na Kashi 93 daga cikin yawan mutanen da suka kama cutar a duniya a shekaran 2018 sannana 2017 yanki ta samu Kashi 94.

Najeriya, Jamhuriyyar kasar Kongo, Uganda, Côte d’Ivoire, Mozambique da Niger na jerin kasashen 10 da cutar ta yi wa katutu a Nahiyar Afrika a 2018.

Yaduwar cutar a lokacin damina.

Ya’u ya ce zazzabin cizon sauro ya fi yaduwa a lokacin damina domin a wannan lokaci asibitoci ke samu marasa lafiya da dama sannan kuma cutar ke yaduwa.

Ya yi Kira ga iyaye da masu kula da Yara da su gaggauta kai ‘ya’yan su asibiti a duk lokacin da aka ga alamun cutar a jikin yaro.

Ya’u ya ce rashin kai yara asibiti da wuri na daga cikin abubuwan dake kashe su.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button