Addini
Ziyarar Ta’aziyya: Kwankwaso Ya Ziyarci Malam Kabiru Gombe.
Tsohon Gwamnan Jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya ziyarci Malamin Addunin Isalama Kuma Sakataren Ungiyar Izala ta Kasa, Sheik Kabiru Haruna Gombe, domin Jajanta masa bisa rasuwar Mahaifiyarsa.
Cikin wadanda Suka Tarbi Kwankwaso Hadda Shugaban Ungiyar Izala ta Kasa Sheik Abdullahi Bala Lau, da Sauran Malaman Izala da Dama.
Kwankwaso ya yi Addu’ar Allah ya Mata Rahama Ya Kyautata Makwancinta.
Iyalai da ‘Yan Uwa da Ta bari Allah Ya basu Hakuri da Juriyar Rashinta, Idan Tamu tazo Allah Yasa mucika da kyau da Imani.
Ahmed T. Adam Bagas