Labarai

Zullum Ya Rabawa ‘yan Gudun Hijira kudi naira Milyan dari da Sha biyar N115m a Dikwa.

Spread the love

Gwamnan Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum ya kwashe Tsawon Ranar alhamis a Dikwa, domin lura da yadda ake rarraba tsabar kudi da nau’ikan abinci ga mata masu rauni da kuma magidanta mutun 34,000.

Matan mutun 23,000, sun karbi kudi naira dubu biyar biyar N5,000 daga jimillan kudin N115m, yayin da magidanta maza dubu 11,000 kowannensu aka ba su shinkafa, buhun wake, buhun masara, da man girki.

Wannan tallafin wani bangare ne na ci gaba da kokarin tallafawa al’ummomin marasa karfi wadanda ayyukan Boko Haram suka hana su Zama a gidajen su da kuma hana masu tayar da kayar baya iya amfani da abubuwan da suka shafi tattalin arziki kamar abinci da tsabar kudi, don diban mayaka daga al’ummomin da suke talautawa.

Bayan kammala aikin agaji ga mazauna garin Dikwa, Zulum ya ziyarci babban asibitin su da kuma wata cibiyar kula da lafiya ta farko, duk a garin na Dikwa.

Yana ba da umarnin likitoci na musamman don kai dayki ga CJTF

A halin da ake ciki, Gwamna Babagana Umara Zulum ya ba da umarnin kula da lafiya ta musamman ga masu aikin sa kai tara a cikin Civilian JTF da Boko Haram ta kai wa hari a Dikwa, ciki har da tashi da su zuwa kasashen waje idan likitoci suka bayar da shawarar hakan.

‘Yan agajin wadanda ke cikin wasu dubunnan, wadanda ke taimaka wa sojoji a yakin da suke yi da Boko Haram, sun samu munanan raunuka tare da wasu
daga gare su suna kwance kafafuwansu sun gurgunta

Kafin likitocin na musamman, Gwamna Zulum ya amince da sake duba kashi 100% na alawus-alawus na wata-wata ga ‘yan agaji tara don inganta lafiyar su.

Zulum ya jinjina musu da kuma wasu da yawa a cikin sadaukar da kai na bayar da gudummawa a ci gaba da hada karfi da karfe don kawo karshen hare-haren kungiyar Boko Haram a cikin sassan jihar Borno.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button