Zulum Namijin Duniya: Harin Da Aka Kai Masa Bai Sa Ya Koma Gida Ba, Ya Cigaba Da Aikin Da Yakeyi Na Rabon Kayan Agaji.
Babu shakka idan kana neman jarumin gwamna adali mara tsoro to kanemi gwamnan jihar Borno Prop. Babagana Umaru Zulum.
A jiya laraba bayan harin da aka kaiwa gwamnan wanda yayi sanadin jikkatar mutune 15 gwamnan ya dora da tafiyarsa zuwa inda ya nufa ba tare da fargaba ba.
Hakan na nuni da cewa ko kadan gwamnan bai razana ba. Duk cewar shi bai taba aikin damara ba, amma kuma yana da dakakkiyar zuciya irin ta Sojoji.
Yawancin gwamnoni idan ana ta’addanci a yankunansu tsoron zuwa ko kusa da garin suke, alal misali: kwanakin baya gwamnan Katsina ya ce tsoro ne yake hanashi zuwa gaisuwar wadanda ‘yan ta’adda suke kashewa a jiharsa.
Shiko gwamna Zulum a koda yaushe da zaran ance masa ankai hari a waje nan take yake tafiya wajen komai dare.
Babu shakka gwamna Zulum Jarumin Jarumai ne…