Labarai

Zulum ya roki Buhari da ya taimaka wa ‘yan gudun hijira mutun 200,000 da su dawo gida Najeriya.

Spread the love

Gwamnan Borno, Farfesa Babagana Zulum, ya roki Gwamnatin Tarayya da Shugaba Muhammadu Buhari daya taimaka wa ‘yan gudun hijirar Nijeriya kimanin mutun Dubu dari biyu 200,000‘ yan asalin Borno dakw kasashen Jamhuriyar Nijar, Kamaru da Chadi don komawa gidajensu

Mista Zulum ya yi wannan rokon ne a Abuja ranar Juma’a a sakonsa na fatan alheri a taron masu ruwa da tsaki kan Aiwatar da Yarjejeniyar ta Duniya kan ‘Yan Gudun Hijira.

Ya bayyana taron a matsayin abin yabo da yabawa.

“‘ Yan gudun hijirar, wadanda yawansu ya kai kimanin 200,000 ‘yan asalin Borno, wadanda ke zaune a kasashen Kamaru, Chadi da Nijar sun nuna aniyarsu ta komawa gida. Sun daɗe suna jiran Ranar da za’ace dasu su dawo gida

Gwamnan ya Kara da Cewa “A zahiri, hakinsu Yana kan wuyana na komawa dasu gida. Ina rokon Gwamnatin Tarayya da ta taimaka. Gwamnatin Borno a shirye take ta hada hannu da Gwamnatin Tarayya ta hanyar Ma’aikatar Harkokin Jin Kai.

“Zamu iya yin hakan da nufin gano wuraren da suka dace don dawosu ta hanyar da ta dace,” in ji Mista Zulum.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button