Tsaro

Zulum ya ziyarci Asibitin koyarwa na Jami’ar Maiduguri ya yi jawabi ga mafarautan da suka samu rauni sakamakon fashewar nakiya a Borno.

Spread the love

Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum ya kasance a asibitin koyarwa na jami’ar Maiduguri a ranar Asabar domin ganin mafarautan guda shida da suka samu raunika sakamakon binne nakiyar da ‘yan ta’addan Boko Haram suka yi a hanyarsu a dajin Sambisa.

Idan za a iya tunawa, mafarauta bakwai sun mutu sakamakon harin nakiya, yayin da aka kawo wasu 16 don yi musu magani a asibiti.

Gwamna Zulum ya dawo daga Abuja ne a ranar Asabar bayan ya halarci wata ganawar sirri da Shugaba Muhammadu Buhari, Ministan Harkokin Waje, Geoffrey Onyeama da Darakta Janar na NEMA, Air Vice Marshall Muhammadu Muhammad (Rtd) kuma kai tsaye ya je ya ga wadanda abin ya shafa.

Kwamishinan wasanni da karfafawa, Hon. Sainna Buba, wacce ta yi wa gwamnan rakiya yayin ziyarar ta ce, 11 daga cikin 16 da suka jikkata an sallame su bayan sun samu kulawa a asibitin koyarwa na jami’ar Maiduguri.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button