Addini

Zuwa Da’awa garuruwan Fulani da Dr. Ahmad Gumi yafara ita ce hanya ce mafi sauki ta magance ta’addanci, in ji Arewa Media Writters.

Spread the love

Kungiyar “Arewa Media Writers” Tana Jinjinawa Sheikh Dakta Ahmad Gumi, Bisa Shiga Kauyukan Fulani Dan Musu Nasiha Akan Ta’addacin Da Ake Yi A Yankin Arewa

….Haka zalika Kungiyar tana bada shawara ga sauran malaman Addinan kasar nan dasu dinga shiga kauyuka, lunguna da sako don kira ga aikata kyakykyawan aiki tare da jawo hankulan al’ummar dake rayuwa a yankunan kan hani ga mummunan aiki

Daga Kungiyar Arewa Media Writers

Kungiyar Marubutan Arewa a kafofin sadarwar zamani “Arewa Media Writers” karkashin jagorancin shugaban kungiyar na kasa Comr Abba Sani Pantami, tana jinjinawa babban malamin addinin Muslunci kuma babban limamin masallacin Sultan Bello dake jihar Kaduna, Sheikh Dakta Ahmad Abubakar Gumi, akan hanyar da ya dakko dan kawo karshen ta’addacin dake faruwa a Nijeriya musamman yankin arewa.

Duba da yadda kullum ake zubar da jinin al’umma da basuji ba basu gani ba, garkuwa da mutane ƙara yawaita yake, kullum cikin kashe-kashen al’umma, musamman a yankin Arewa kara ta’zzara yake, ba yaro babu babba.

Wannan dalilin ne yasa Dakta Gumi ya fara shiga lungu da sakon ƙauyuka, da karkara tare da jawo hankalin al’ummar dake rayuwa a yankunan, kan muhimmancin Ran dan Adam, a bayan kasa zai kawo karshen lamarin ko rage faruwan haka, kuma yawanci in kaji anyi ta’addan ci, zaka tarar ƙabilar Fulani sukayi musamman ma a nan yankin Arewa.

Dakta yace dalilin shi kuwa shi ne, duk sanda kaji ance anyi ta’addanci zaka ga Fulani ne, suka yi, kuma yana ganin cewa rashin zuwa a musu da’awa ne, a gaya musu abun da Allah SWA yace akan zubda jini, da kuma sanin makomar mai kashe Rai ba tare da hakki ba zai kasance yasa suke aikata hakan.

Haka zalika Kungiyar “Arewa Media Writers” tana bada shawara ga sauran malaman addinin kasar nan da sarakuna suyi koyi da hanyar da Dakta Gumi ya dakko dan kira da kyakkyawan aiki da kuma hani da mummunan aiki.

Kungiyar tace a wannan lokacin ya kamata malaman addinin Islama dana Kirista su kauda banbance-banbancen Addini da aqida da ra’ayi, suyi Amfani da murya daya wajan shiga ƙauyuka don kiran al’umma dan sanar dasu abun da ya kamata suyi a zamansu na duniya.

Kungiyar tace domin su yan ta’addan in sukazo ta’addanci ba ruwan su da yaren ka, ko addinin ka, ko yankin ka, dan haka muna kira da azo a hada kai a yaki wannan taaddancin.

Allah SWA ya kawo mana zaman lafiya mai daurewa a yankinmu na Arewa dama kasar mu Nijeriya. Amin

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button