Kasashen Ketare

Zuwa Karshen Shekara Za A Sami Rigakafin Covi-19, Dr. Fauci Ya Fadawa Majalissar Dokokin Amurka.

Spread the love

Kwararre a fannin cututtuka masu yaduwa na Amurka Dr Anthony Fauci ya fadawa ‘yan majalisar dokokin Amurka a jiya Juma’a 31 ga watan Yuli cewa ya na da kwarin gwiwa za a samar da rigakafin cutar coronavirus nan da ‘yan watanni masu zuwa, yayin da cutar ke cigaba da bazuwa a kasar.

“Muna sa ran daga nan zuwa karshen shekara, zamu samu rigakafin da zamu iya cewa ya na aiki kuma bai da illa, abinda Fauci ya fada kenan a gaban wani kwamitin majalisar wakilai da ke bincike akan coronavirus.

Fauci ya ce a kwanan nan aka shiga mataki na karshe cikin matakai 3 na gwajin rigakafin.

A jawabin bude zaman, shugaban kwamitin na jam’iyyar Democrat James Clyburn da dan jam’iyyar Republican Steve Scalise, sun tafka muhawa akan ko gwamnatin Trump na da wata dabara ta magance annobar coronavirus ko a’a.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button