Tsaro

Wasu ƙasurguman ‘yan Bindiga guda 4 aka saki kafin a sako Ɗaliban Makarantar Sakandiren Kagara ta Jihar Neja.

Spread the love

Gwamnatin Jihar Neja a jiya ta shaidawa manema Labarai cewa ba a biya kudin fansa ba don sakin yaran da abin ya shafa, Kwamishinan yaɗa Labarai Na Jihar Neja Alhaji Muhammad Sani Idris kuma ya daɗa tabbatar da cewa, babu musanyar fursunoni wajen sakin yaran, kawai anyi amfani da wasu dabarun gwamnati ne wajen kuɓutar da Ɗaliban.

Amma wata majiya data bukaci a boye sunanta ta bayyana cewa wasu ƙasurguman ‘yan Bindiga gwamnatin Neja ta saki sannan aka sakko Ɗaliban, majiyar ta ce yanzu an sakar musu guda 2 sannan nan gaba kaɗan za a kammala shirin da za a sakar musu ragowar guda 2.

A lokacin da gwamnatin Neja ke kokarin ganin ta kuɓutar da Ɗaliban, ta yi amfani da wani ɗan Bindiga wajen isa ga shugaban ƙungiyar mai suna Kachalla, daga bisani ya hau Babur inda yayi tafiya har tsahon awanni tara domin yaje ya haɗu da kachalla shugaban masu garkuwar.

Majiyar ta kara da cewa shi wannan Ɗan Bindigar ya shawo kan kachalla don ya bada damar asaki wadanda aka sace duk da cewa ba duk mutanen da sukeso bane gwamnatin ta sakar musu.

Bayan kwanaki da Ɗan Bindigar ya shafe yana zarya tsakanin gwamnatin Neja da shugaban ƙungiyar masu garkuwa da mutanen mai suna kachalla, an saki waɗanda aka sace ga hukumar ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro da misalin karfe 7 Na safiyar Asabar.

Daga Kabiru Ado Muhd

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button